‏ Matthew 19:1-12

Kashen aure

(Markus 10.1-12)

1Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun. 2Taron mutane mai yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.

3Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?”

4Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’
Far 1.27
5ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?
Far 2.24
6Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”

7Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?”

8Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. 9Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”

10Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.”

11Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu. 12Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.”
Copyright information for HauSRK