Matthew 21:1-11
Shigar mai nasara
(Markus 11.1-11; Luka 19.28-38; Yohanna 12.12-19)
1Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.” 4Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa, 5“Ku ce wa Diyar Sihiyona,‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,
mai tawali’u yana a kan jaki,
a kan aholaki, ɗan jaki.’ ” ▼
▼Zak 9.9
6Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. 8Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. 9Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ▼
▼Wani faɗi na Ibraniyanci mai ma’anar “Ceto!” Wanda ya kasance wani salon yabo; haka kuma a aya 15
ga Ɗan Dawuda!”“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” ▼
▼Zab 118.26
“Hosanna a cikin sama!”
10Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?” 11Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”
Copyright information for
HauSRK