Matthew 21:20-22
20Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?” 21Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru. 22In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”
Copyright information for
HauSRK