Matthew 22:15-22
Biyan haraji ga Kaisar
(Markus 12.13-17; Luka 20.20-26)
15Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa. 16Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba. 17To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?” 18Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? 19Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari, 20sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?” 21Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.” 22Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.
Copyright information for
HauSRK