‏ Matthew 22:23-33

Aure a tashin matattu

(Markus 12.18-27; Luka 20.27-40)

23A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya. 24Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan’ya’ya. 25A cikinmu an yi’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa. 26Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai. 27A ƙarshe, macen ta mutu. 28To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?”

29Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba. 30Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama. 31Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne, 32‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’
Fit 3.6
? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”

33Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
Copyright information for HauSRK