Matthew 22:41-46
Kiristi, ɗan wane ne?
(Markus 12.35-37; Luka 20.41-44)
41Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su, 42“Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.” 43Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce, 44 “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,“Zauna a hannun damana,
sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.” ’ ▼
▼ Zab 110.1
45 To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?” 46Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.
Copyright information for
HauSRK