‏ Matthew 24:15-21

(Markus 13.14-23; Luka 21.20-24)

15 “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’
Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11
wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),
16to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. 17Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida. 18Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa. 19Kaiton mata masu ciki da mata masu renon’ya’ya a waɗancan kwanakin! 20Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. 21Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.
Copyright information for HauSRK