‏ Matthew 24:36-44

Rana ko sa’a ba a sani ba

(Markus 13.32-37; Luka 17.26-30,34-35)

36 “Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 38Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; 39ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 40Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. 41Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.

42 “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. 43Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida. 44Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.
Copyright information for HauSRK