Matthew 24:37-41
37Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 38Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; 39ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 40Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. 41Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
Copyright information for
HauSRK