‏ Matthew 24:45-51

(Luka 12.35-48)

45 “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci? 46Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. 47Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa. 48Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49Sa’an nan yă fara dūkan’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.
Copyright information for HauSRK