Matthew 26:1-5
An ƙulla shawara gāba da Yesu
(Markus 14.1,2; Luka 22.1,2; Yohanna 11.45-53)
1Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, 2“Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.” 3Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas, 4suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi. 5Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”
Copyright information for
HauSRK