‏ Matthew 26:31-35

Yesu ya yi maganar mūsun da Bitrus zai yi

(Markus 14.27-31; Luka 22.31-34; Yohanna 13.36-38)

31Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin,
tumakin garken kuwa za su fasu.’
Zak 13.7

32 Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

33Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”

34Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”

35Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
Copyright information for HauSRK