Matthew 26:36-46
Getsemane
(Markus 14.32-42; Luka 22.39-46)
36Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.” 37Ya ɗauki Bitrus da’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu. 38Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.” 39Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.” 40Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba? 41Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.” 42Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.” 43Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci. 44Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda. 45Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi. 46Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
Copyright information for
HauSRK