‏ Matthew 26:57-68

A gaban majalisa

(Markus 14.53-65; Luka 22.54,55,63-71; Yohanna 18.13,14,19-24)

57Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru. 58Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.

59Sai manyan firistoci da’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi. 60Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito.

A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

62Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?” 63Amma Yesu ya yi shiru.

Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”

64Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”

65Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon. 66Me kuka gani?”

Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”

67Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi 68suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
Copyright information for HauSRK