Matthew 26:6-13
An shafe Yesu a Betani
(Markus 14.3-9; Yohanna 12.1-8)
6Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, 7wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci. 8Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! 9Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.” 10Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne. 11Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba. 12Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata. 13Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
Copyright information for
HauSRK