‏ Matthew 27:45-56

Mutuwar Yesu

(Markus 15.33-41; Luka 23.44-49; Yohanna 19.28-30)

45Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka. 46Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi,
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Eloi, Eloi
lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
Zab 22.1

47Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”

48Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha. 49Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”

50Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.

51A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. 52Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi. 53Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

54Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”

55Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima. 56A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar’ya’yan Zebedi.
Copyright information for HauSRK