‏ Matthew 27:57-61

Bizinar Yesu

(Markus 15.42-47; Luka 23.50-56; Yohanna 19.38-42)

57Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. 58Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi. 59Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta. 60Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa. 61Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.
Copyright information for HauSRK