Matthew 5:38-48
Ramuwa
(Luka 6.29,30)
38 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’ ▼▼ Fit 21.24; Fir 24.20; M Sh 19.21
39Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma. 40In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma. 41In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu. 42Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka. Ƙauna don abokan gāba
(Luka 6.27,28,32-36)
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ▼▼ Fir 19.18
ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba suna da abokan gāba, ku sa wa waɗanda suke la’antarku albarka, ku yi wa waɗanda suke ƙinku alheri
kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45don ku zama’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47In kuwa kuna gai da’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.
Copyright information for
HauSRK