Matthew 6:9-13
9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a. “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,a tsarkake sunanka,
10 mulkinka yă zo
a aikata nufinka a duniya
kamar yadda ake yi a sama.
11 Ka ba mu yau abincin yininmu.
12 Ka gafarta mana laifofinmu,
kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.
13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,
amma ka cece mu daga mugun nan. ▼
▼ Ko kuwa daga mugu ; waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba ɗaya, gama mulki da iko da ɗaukaka naka ne har abada. Amin.
’
Copyright information for
HauSRK