Matthew 8:19-22
19Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.” 20Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” 21Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.” 22Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”
Copyright information for
HauSRK