Matthew 8:28-34
Warkar da mutum biyu masu aljanu
(Markus 5.1-20; Luka 8.26-39)
28Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Gergesenawa; waɗansu kuma Gerasenawa ne a nan
(ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. 29Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi? 30Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. 31Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” 32Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. 33Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. 34Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki.
Copyright information for
HauSRK