Numbers 20:22-29
Mutuwar Haruna
22Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor. 23A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 24“Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba. 25Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor. 26Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.” 27Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a. 28Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen, 29sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.
Copyright information for
HauSRK