Numbers 21:21-30
An ci Sihon da Og
(Maimaitawar Shari’a 2.26-37)
21Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce, 22“Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.” 23Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila. 24Isra’ila fa suka kashe shi da takobi, suka ƙwace ƙasarsa, tun daga kogin Arnon har zuwa kogin Yabbok, zuwa kan iyakar Ammonawa kawai, gama sun yi wa iyakansu katanga. 25Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta. 26Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon. 27Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce, “Ku zo mu sāke gina Heshbon,birnin Sihon.
28“Mayaƙansa sun fito kamar
harshen wuta
suka ƙone birnin Ar na Mowab
suna hallaka’yan ƙasar
tuddan Arnon.
29Kaitonki, Mowab!
Gunkinki Kemosh
ya yashe mutanenki;
aka kuma kama su, aka kai su bauta
wajen Sihon sarkin Amoriyawa.
30“Amma mun tumɓuke su,
mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon.
Mun ragargaza su har zuwa Nofa
wanda ya miƙe zuwa Medeba.”
Copyright information for
HauSRK