Numbers 28:16-25
Bikin Ƙetarewa
(Firistoci 23.4-8)
16“ ‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari. 17A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti. 18A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba. 19Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji. 20Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; 21da kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 22A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara. 23Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya. 24Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha. 25A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba.
Copyright information for
HauSRK