‏ Numbers 28:26-31

Bikin Makoni

(Firistoci 23.15-22)

26“ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. 27A miƙa hadaya ta ƙonawa da’yan bijimai biyu, rago ɗaya da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 28Da kowane bijimi a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; 29da kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 30A haɗa da bunsuru guda don yin muku kafara. 31A miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha, haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadayarta ta sha. A tabbata dabbobin nan marasa lahani ne.
Copyright information for HauSRK