Numbers 29:7-11
Ranar Kafara
(Firistoci 23.26-32)
7“ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba. 8Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma’yan raguna bakwai,’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 9Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; 10kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 11A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.
Copyright information for
HauSRK