Psalms 105:1-15
1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
2Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
3Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
4Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
5Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,
mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,
6Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa,
Ya ku’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.
7Shi ne Ubangiji Allahnmu;
kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya.
8Yana tuna da alkawarinsa har abada,
maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
9alkawarin da ya yi da Ibrahim,
rantsuwar da ya yi wa Ishaku.
10Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida,
Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,
11“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana
a matsayin rabo za ka yi gādo.”
12Sa’ad da suke kima kawai,
kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
13suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,
daga masarauta zuwa wata.
14Bai bar kowa yă danne su ba;
saboda su, ya tsawata wa sarakuna,
15“Kada ku taɓa shafaffena;
kada ku yi wa annabawa lahani.”
Copyright information for
HauSRK